wane-ƙoƙari-gwamnatin-shugaba-buhari
Wane ƙoƙari gwamnatin shugaba Buhari ta ke yi don haɓaka tattalin arzikin ƙasa?
6 views
Bajekolin Alheri
16 subscribers
Published on Apr 18, 2021
Idan za a kwatanta da sauran:
Tsarin tattalin arzikin Buhari ya yi wa nasu fintinkau
Nijeriya tana sahun gaba a jerin kasashen da suke da dimbin albarkatun kasa, kuma daga baqin zinare (black gold) da kasar noma, da tarin ma’adinai babu iyaka.
Amma, ita kanta wanzuwar kasa ita ce ginshiqin samun tsarin tattalin arzikinkasa, ma’ana idan babu qasa mai cike da yawan jama’a, galibi masu hangen nesa da dattako, zancen a yi maganar tattalin arzikin kasa bai taso ba.
Shugaba Muhammadu Buhari ya karɓi jan ragamar mulkin Nijeriya , a shekara ta 2015, a daidai lokacin da manyan kasashe masu faɗa-a-ji irin su Ingila da Amirka suka yi hasashen wargajewar kasar, kowa ya kama gabansa, amma ina! Jarmai Buhari ya kawar da kowace irin fargaba, Nijeriya ta ci gaba da kasancewa dunkulalliya, mai ‘yanci da cikakken mulkin kai, abin da ya kunyata manyan kasashen duniya, da baqar aniyarsu, duk an manta.
A nan, za a iya fahimta karara cewa, tattalin arziqin kasa ya ginu ne a kan wanzuwar qasar tun da farko, kafin a kai ga maganar samun arziki da wadata daga bangaren gwamnati, da xaixaikun mutane mawadata, da kuma akasin haka.
Wani marubuci kuma ganau, Mista Abraham Isaac Adigun ya yi bayani daki-daki cikin wata makalar da ya rubuta, inda yake cewa, duk da biliyoyin dalar Amirka da gwamnatin PDP ta samu, ba ta iya gina matatar mai ko daya ba, ba ta sami zarafin yaki da Boko-Haram ba, ta kasa biyan albashi, ma’ana Kanar Sambo Dasuqi da Dokta Okonjo Iweala sun gaza kai bante a wuraren da ke karqashin kulawarsu, tsaro da sha’anin kudi, duk da cewa, farashin man fetur ya yi tashin gwaron zabo, zuwa dalar Amirka 100.
Zakakurin marubucin, Adigun ya ci gaba da yin bayani dalla-dalla kamar haka, daga shekara ta 2016 zuwa 2019, gwamnatin Nijeriya ta rarraba wa rukunin gwamnatoci uku da ake da su, majalisun qananan hukumomi, da jihohi da tarayya har dala biliyan 73 da xigo 40, a yayin da a shekara xaya rak, watau a shekara ta 2013, gwamnatin Jonathan ta yi awon gaba da dala biliyan 74, fiye da lissafin da ya gabata, domin daga shekara ta 2015 har zuwa 2017 gwamnatin Buhari ta rarraba wa rukononin gwamnatoci gaba xaya dala biliyan 71 da xigo 4.
Wani lissafin ya tabbatar da cewa, gwamnatin Jonathan ta tara kuxin shiga har dala biliyan 260, a duk da haka, rance ta yiwo daga qasar Sin, ta biya kudin gina hanyar jirgin qasa (dogo) daga Abuja zuwa Kaduna, idan aka kwatanta da yadda har zuwa yau xin nan, gwamnatin Buhari ta ranto dala biliyan 20 kacal.
Gwamnatin Jonathan ta wawashe asusun ajiyar kasashen waje, ta yi masa tatas, bayan wanda ya gada ya bar masa fiye da dala biliyan 60, a saboda karyewar darajar Naira, babu ruwan gwamnatin Buhari, domin ba ita ta kar zomon ba, rataya aka ba ta.
Har ila yau, akwai kasar Aljeriya, ya kamata a bayar da misali da ita, domin a daidai lokacin da farashin mai ya tashi zuwa dala 100, ita ta sami zarafin cika lalitarta zuwa dalar Amirka biliyan 190, Nijeriya kuwa ko sisi.
Duk da ximbin kudaden da Nijeriya ta samu a lokacin Jonathan, a maimakon a gina matatar mai, da asibitoci masu matsayi na duniya, da hanyar jirgin qasa, da gadoji da kuma makarantu, a maimakon haka sai daure wa cin hanci da rashawa gindi kawai ta lakanta. A hankalce, ta yaya wanda ya kwashe shekaru 16 a kan karaga, ya kasa gina asibiti mai matsayi na duniya, wanda ya shekara 6 kacal zai iya ginawa?
Duk da wargajewar tsarin tattalin arziqin da gwamnatin Buhari ta gada daga gwamnatin PDP, ta sami zarafin kammala gina hanyar jirgin qasa, daga Abuja zuwa Kaduna, kuma ta qaddamar da gina hanyar jirgin qasa, wadda za ta ratsa Kano da Jigawa zuwa Maraxi da ke Jamhuriyar Nijar.
Waɗansu ayyukan raya qasa na bajinta da gwamnatin Buhari ta qaddamar sun haxa da titin Kano zuwa Katsina, da amincewa da sake gina titin Kabuga zuwa Gwarzo, ya zarce zuwa Dayi, cikin jihar Katsina.
Baya ga ayyukan raya kasa birjik, a sassan Nijeriya, Kudu da Arewa, gwamnatin Buhari ta qaddamar da shirin bayar da tallafi ga xaixaikun mutane, da kuma ‘yan kasuwa, mayansu da kanana, tare da gagarumin shirin nan nata na yaqi da zaman-kashe-wando, inda ta qaddamar da daukar ma’aikata matasa aiki, su 774,000 ma’ana, kowace qaramar hukuma da ke faxin tarayyar Nijeriya za ta samu matasa 1000 waxanda za su ci gajiyar shirin.
A nan, babu inda-inda, masana tsarin tattalin arzikin kasa irin su Farfesa Sa’idu Ahmad Dukawa, na jami’ar Bayero Kano, da Alhaji Amanallah Ahmad Muhammad Getso, tsohon shugaban karamar hukumar Tarauni, da Farfesa Kamilu Sani Fagge daga jami’ar Bayero Kano, da Alhaji Sani Ya’u Vavura, da Dokta Usman Muhammad Jahun na bangaren tsaro, da Alhaji Nura D.O Ma’aji, da Farfesa Binta Tijjani duk sun tofa albarkacin bakunansu wajen jinjina wa kokarin gwamnatin Buhari, ta fuskokin tsaro, da tattalin arzikin kasa, da yaqi da cin hanci, da karbar rashawa. Sun yaba, kuma sun bayar da shawarwari
...
https://www.youtube.com/watch?v=wYOJlQr2bb0
Transaction
Created
3 weeks ago
Content Type
Language
video/mp4
ha